• Labaran yau


  Wani dan kwallo ya fadi ya mutu ana tsaka da wasa


  Wani matashin dan kwallon Najeriya, da aka bayyana da sunan Damilola a jihar Osun ya bayyana ya fadi ya mutu ana tsaka da wasan kwallon kafa ranar 7 ga watan Satumba.


  Lamarin ya farune a yankin Ido dake jihar yayin da yakewa kungiyarsa ta Club Ofatedo wasa, ya bugawa wani kwallo kawai sai ya fadi kasa, nan aka hanzarta dashi Asibiti inda Likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

   

  Abokan wasansa sun ce bai nuna wata Alamar rashin Lafiya ba kamin su fara buga kwallo.

   

  Shugaban kungiyar matasan ‘yan kwallo na jihar, Leke Hamzat ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

  Hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani dan kwallo ya fadi ya mutu ana tsaka da wasa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama