Faɗa a gidan yari: Fursuna ya datse yatsun gandireba ya haɗiye a Italy


Wani shugaban kungiyar miyagu da aka yi wa ɗaurin rai da rai a gidan yari ya gutsure yatsun gandireba ya haɗiye yayin faɗa kamar yadda wata kafar watsa labarai na Italiya ta ruwaito.

Guiseppa Fanara mai shekaru 60 da aka yi wa ɗaurin rai da rai a gidan yarin Rebibbia a ƙasar Rome ya kai wa masu gadin gidan yari bakwai hari a watan Yuni da suka shigo dakinsa yin bincike kamar yadda Daily Il Messagero ta ruwaito.

A halin yanzu Fanara wadda ɗan kungiyar Mafiya ta Cosa Nostra ne yana shekararsa ta tara kenan a gidan yarin na ƙasar Italiya.

Saboda hatsarin da ke tattare da mutane irinsa, a kan ware su daban ne a gidan yarin a basu ɗaki su kadai domin hana su cigaba da aikata laifuka daga cikin gidan yarin inda suka hulda da sauran fursunoni.

"Yayin fadar da suka yi, Fanara ya yi amfani da haƙoransa ya guntule ƙaramin yatsan gandireban na hannun dama," a cewar jaridar.

"Sai dai an kasa gano ɗan yatsar hakan yasa wani mai bincike a kasar ta Rome ya cimma matsayar cewa an haɗiye yatsar ne," jaridar ta kara da cewa.

Daga nan sai Fanara ya yi wa sauran masu gadin gidan yarin shida barazana da tsinke da ya ke rike a hannunsa inda ya ce, "zan yanka wuyan ku kamar aladai!"

Tuni dai mayar da Fanara wani gidan yarin a mai tsauraran matakan tsaro a Sardina inda ake tuhumar sa da sabbin laifuka da suka hada da faɗa da rashin yarda a kama shi.

A farkon wannan shekarar kasar Italy ta yi niyyar sakin wasu tsaffin shugabannin kungiyar miyagu ciki har da ƴan Cosa Nostra.

Amma al'ummar ƙasar sun nuna ƙin amincewarsu hakan dole ma'aikatar Shari'a kasar ta dakata da batun ta ce za ta sake bita.

A wani rahoton, kun ji cewa a ƙalla hausawa 2 mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka mutu sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.

Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN