• Labaran yau


  ‘Yan ta’adda sun kwacewa ‘yansandan Najeriya Bindiga sun kashe mtum 1


  Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa, ‘yan ta’adda a Egbu dake Owerri da Owerre Nkworji dake karamar hukumar Nkwerre sun kaiwa ‘yansanda hari inda suka kwace musu bindigu da kuma daddatsa daya daga ciki wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.


  Ranar Litinin ne ‘yan Bindigar suka kaiwa ‘yansandan dake Nkwerre hari inda suka daddatsa daya daga ciki sannan suka kona motar aikin ta ‘yansandan.

   

  An garzaya da wanda aka sara Asibiti ranar Talata saidai daga baya ya rasu, kamar yanda Rahoton Punch ya tabbatar.

   

  Hakanan kuma wasu ‘yan Bindigar sun kai wa ‘yansanda hari a Egbu inda suma suka kwace musu bindigu da sarar wani dansanda amma daga baya an garzaya dashi Asibiti.

   

  Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Isaac Akinmoyede da aka tuntubeshi ya tabbatar da cewa, an kwacewa ‘yansandan Bindigu amma babu wanda aka kashe

  Hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: ‘Yan ta’adda sun kwacewa ‘yansandan Najeriya Bindiga sun kashe mtum 1 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama