'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara


Jami'an 'yan sanda a jihar Zamfara sun damke wani mutum mai suna Abu Dan-Tabawa, makusancin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, bayan da yake taron sirri da wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an kama Dan-Tabawa ne bayan rahoton da aka samu daga na'urar nadar hoto da Gwamna Bello Matawalle ya saka a dukkan fadin babban birnin Gusau.An gano cewa, a halin yanzu Dan-Tabawa yana amsa tambayoyi a hannun 'yan sandan jihar. Daily Nigerian ta wallafa cewa, rundunar 'yan sandan na kokarin sakin wanda ake zargin sakamakon wani umarni da ake zargin ya zo daga Abuja. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya tabbatar da cewa Dan-Tabawa ya shiga hannun jami'an tsaron tare da wasu mutum 17 da ake zargi.Kakakin rundunar 'yan sandan, a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce kamen bashi da wata alaka da siyasa. Ya ce: "Kamen ya samo asali ne daga bayanan sirrin da aka samu kuma rundunar 'yan sandan tana yin iyakar kokarina wurin ganin cewa ba a yi karantsaye ga zaman lafiya ba a jihar. "An yi kamen ne domin bai wa dukkan jama'ar jihar da yankin baki daya tsaro."Rundunar tana sanar da dukkan jama'ar jihar da su guji fadawa cikin kowanne al'amari da zai zama kalubale ga tsaro, komai kuwa girma ko darajar su." Shugaban jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Alh. Ibrahim Bilal, ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a garin Yola kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN