Attahiru Jega ya aika wa Buhari sako cewa talakawa na shan bakar wahala


Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega; da tsohon shugaban malaman Katolika a Abuja, Cardiac John Onaiyekan, sun yi martani kan halin da jama’a ke ciki. Sun fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yan Najeriya na fuskantar wahala biyu na rashin tsaro da kuma na annobar coronavirus.



Don haka sun yi kira ga Shugaban kasar da ya yi duk abunda zai iya domin magance matsalar tsaro koda hakan na nufin sallamar shugabannin tsaro. Sun bayyana hakan a cikin wani jawabi mai taken, ‘Ya shugaban kasa, Gwamnoni: Yanzu ne lokacin tattaunawa’ a ranar Lahadi. Jawabin na dauke da sa hannun Jega, Onaiyekan, Janar Martin Agwai, Amb. Fatima Balla, Farfesa Jibrin Ibrahim, Misis Aisha Muhammed-Oyebode, Dr. Nguyan Feese. Sai Dr. Usman Bugaje da Dr. Chris Kwanja, dukkaninsu mambobin kungiyar Najeriya kan zaman lafiya da shugabanci nagari ne.



Jawabin ya zo kamar haka: “Najeriya, kamar dukkanin kasashen duniya tana fama da annobar korona. Sai dai, al’umman Najeriya na fuskantar wahala biyu ne saboda suna kuma fama da rashin tsaro da rikici a fadin kasar. “Ya zama dole gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa wajen magance hauhawan rashin tsaro, idan tana son cimma nasara a yaki da annobar. Wani binciken USIP na bayan nan a Najeriya ya gano sabon alaka tsakanin COVID-19, rashin zaman lafiya da kuma rikici.



“Musamman, binciken ya gano cewa wadanda rikice-rikice ya cika dasu ba za su aminta da matakan gwamnati na yaki da annobar korona ba idan aka kwatanta su da wadanda rikicin bai shafa ba. Sun kuma bayar da shawarwari kan yadda gwamnatin Najeriya za ta iya karfafa kokarinta na daidaita annobar ta hanyar magance rashin tsaro a fadin kasar. “Garkuwa da mutane don kudin fansa ya kasance babban abun damuwa a fadin kasar.



Yankin arewa maso gabas na fuskantar fawowar ayyukan Boko Haram, sannan yan bindiga sun mayar da dubban mutane marasa galihu a fadin garuruwan karkara a arewa maso yamma. “Miyagun ayyuka a yankunan karkara na kara tabarbarar da lamarin tsaron abinci, domin manoma da dama basa iya zuwa gonakinsu tsawon watanni da dama saboda tsoron rasa ransu,” in ji kungiyar. Sun yi kira ga Shugaban kasar a kan ya shirya wani tsari na tattaunawa domin magance rikici da ake samu na kabilanci da na addini.



Kungiyar ta ce majalisar kasa a jiha ya jagoranci shirin tattaunawar a matakin kasa yayinda kungiyar gwamnonin Najeriya za ta tabbatar da lamarin ya isa ga talakawa Sun bayyana cewa rikici tsakanin makiyaya da manoma ya yi sanadiyar rasa dubban rayuka a kasar sannan yana kara zurfafa rikicin kabilanci amma yan tsirarun mutane aka hukunta kan haka. Don haka kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta yi umurnin sake bincike a kan dukkanin rikicin makiyaya da manoma na baya. Sun bukaci gwamnati da ta sallami shugabannin tsaro idab hakan ne zai kawo ci gaban abubuwa.



A wani labari na daban, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya ce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar da gudunmawa wajen saka Najeriya a halin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya risketa na tabarbarewa. Jigon kasar na martani ne ga furucin da Obasanjo ya yi a kwanan nan game da gwamnatin Buhari. Tsohon shugaban Najeriyan ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari, kan yanda yake tafiyar da harkokin kasar, inda ya yi gargadin cewa Najeriya na lalacewa cikin sauri a karkashin mulkin Shugaba Buhari.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN