• Labaran yau


  Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan


  Katafaren gidan mawakiya Rihanna da ke birnin London wanda ta kwashe kusan shekaru biyu da rabi ana gina shi an daga shi domin siyarwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa.


  Za a siyar da katafaren gidan a kan pam miliyan 32 wanda yayi daida da Naira biliyan 14, shafin Linda Ikeji ya wallafa. Gidan mai dakin kwana takwas yana nan a St Johns, yana da kofofi biyar manya tare dakin wanka mai kamar wurin gyaran jiki tare da katafaren lambu. 

   

  Katafaren gidan da ke birnin London na da wurin adana motoci har 10, wurin motsa jiki da manyan dakunan nishadi biyu tare da madafi katafare.


  An fara gina gidan a 1844 wanda ya zama mallakin Daniel Francis, babban dan kasuwar lu'u-lu'u. Fitaccen magini William Holme Twentyman ne ya gina. Ga hotunan katafaren gidan.


  Source: Legit


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama