• Labaran yau


  Yan bindiga sun sace diyan Ma'aji su 3, sun kashe mutum 1 a Nahuce, Bungudu jihar Zamfara


  Yan bindiga sun sace diyan Ma'aji Alhaji Yusuf  Marafa su uku, kuma suka bindige makwabcinsa har lahira a mazabar Nahuce da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.


  Wata majiya ta shaida wa jaridar Vanguard ranar Alhamis 10 ga watan Satumba cewa yaran da yan bindigan suka sace sun hada da Mansur Yusuf, Anas Yusuf, da Sa'adu Yusuf, da kuma makwabcinsa Malam Kamalu Nahuce.


  Wani dan asalin garin mai suna Alhaji Dahiru, ya ce " Yan bindigan sun shigo garin ne kan babura da dama kuma suka zarce kai tsaye zuwa gidan Ma'ajin suka sace diyansa guda uku. Sun bindige Alhaji Kamalu ne bayan ya fito daga gidan".


  Haka zalika Dahiru ya ce yan bindigan sun kuma shiga gidan wani dan kasuwa mai suna Ibrahim Maishago, a kokarinsu na sace yaransa, sai suka yi sa'a da wasu kudi masu yawa suka sace kudin suka tafi da su tare da yaran.

   

  Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce an tura jami'an tsaro a yankin domin maido da doka 


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan bindiga sun sace diyan Ma'aji su 3, sun kashe mutum 1 a Nahuce, Bungudu jihar Zamfara Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama