Gwamnatin jihar Kebbi ta fara shirin kai taimako ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar


Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kebbi Alhaji Hassan Muhammed Shell, ya ce Gwamnatin jihar Kebbi tare da kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar sun dukufa wajen ganin sun bayar da agaji ga wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa a fadin jihar.

 

Shella ya shaida wa manema labarai a Birnin kebbi cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta umarci shugabannin kananan hukumomi su tattara sunayen wadanda lamarin ya shafa, tare da hada adadin gidaje, da gonaki da ambaliyar ruwan ya barnata, har da adadin dabbobi.

 

Haka zalika ya yi gargadin cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta ja kunnen shugabannin kananan hukumomi kada su sa son rai wajen tattara bayanai da suka shafi yunkurin bayar da agaji ga jama'a.

 

Ya ce an tanadi yin haka ne domin samar da ingantaccen bayani da Gwamnatin jihar Kebbi za ta yi amfani da shi wajen taimaka wa jama'a da ibtila'in ambaliyar ya shafa.

 

Ya kara da  cewa Gwamnati ta kuma umarci shugabannin kananan hukumomi su tanadi matsugunin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa ta hanyar yin amfani da gine ginen Gwamnati da ake da su a kananan hukumominsu, wadanda suka hada da Makarantun Pramare da na Sakandare, da kuma Asibitoci.

 

An kuma umarci shugannanin kananan hukumomi su samar da ababen tsabtace muhalli da wanda za a yi amfani da su wajen tsabtan jama'a yayin da suke zaune a wajajen da aka tanada masu na gaggawa a kananan hukumomi kafin hukumar bayar da agaji na gaggawa na jihar Kebbi SEMA ta kai kayakin agaji ga jama'a.

 

Shella ya ce Gwamnati ta bukaci kananan hukumomi su binciko kayakin amfanin gona da za a iya shukawa kafin karshen lokacin Damana, wadanda suka hada da Dankali, Rogo, Doya da sauransu.

 

Ya kara da cewa " Gwamnati ta umarci kananan hukumomi su hada gwiwa da NURTW, NARTO, yan sanda da sauran jami'an tsaro domin ganin an kayyade yadda motoci za su dinga bin hanyoyin titi da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan domin kauce wa hadari".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN