Yadda bindigogin sirri ke barazana ga Afghanistan


Jami’an tsaro a Afghanistan sun kama tulin bindigogi masu siffar alkalami da suke zargin ’yan ta’adda da sauran miyagu na amfani da su a yayin da kasar ke fama da kashe-kashen siyasa.

’Yan sanda a birnin Kabul — hedikwatar kasar — mai fama da kashe-kashen siyasa sun ce bindigogin masu daukar harsashi daya-daya ne kuma sunana da wuyar ganewa.

“Bindigogin na da siffar biron da ake dannawa idan za a yi rubutu ta yadda idan mai maharbi ya sa harsashi a ciki zai saita abin da zai harba sannan ya dannan maballin da ke zama a matsayin kunamar bindigar”, inji wani jami’in Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) a Kabul.

A karshen makon jiya ne ’yan sanda suka bankado bindigogi masu siffar alkalami guda 48 a cikin tarin wasu makamai da aka kama da suka hada da bom na likawa a jikin wurare, da ake tayarwar daga nesa.Kakakin Ma’aikatar Tsaron Afghanistan, Tariq Arian ya ce, “’yan ta’addan na so su yi amfani da makaman ne wurin yin kashe-kashe a Kabul”.
  • Tabarbarwar tsaro a Kabul

Karuwar rashin aikin yi da fatara sun kara tsananta matsalar tsaro a birnin mai fama da masu garkuwa da mutane da fashi da kuma harbe-harbe barkatai.

Matsalar ta kara tsanani bayan kashe-kashen siyasa da ake yi wa masu fafutikar zaman lafiya da masana da kuma jami’an gwamanti.

“An kashe akalla mutum 40 a irin wadannan hare-hare a Kabul kadai cikin watanni shidan da suka gabata”, inji jami’in na CID.

Ya ce an yi ta kai hare-haren ne ta hanyar makaman da ba a kai ga ganewa

ba, amma jami’an tsaro na kyautata zaton bindigogi masu fasalin abin rubutu ne.

  • Shin Taliban na da hannu?

Hukumomin kasar na zargin kungiyar Taliban da kungiyoyi masu alaka da ita da kai hare-haren.

Taliban wadda ta shiga yarjejeniya da Amurka a watan Fabrairu bisa sharadin ba za ta rika kai hare-hare ba ta nesanta kanta da hare-haren.

Sai dai hare-haren masu tayar da kayar bayan na ta karuwa a kan jam’ian tsaro a yankunan karkara, yayin da Taliban da gwamnatin Afghanistan ke kan tattaunawa a birnin Doha da Daular Larabawa domin kawo karshen yakin shekara 19 da bangarorin ke yi.

 

Source: Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN