• Labaran yau


  Bayan ya kaura wa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sace yanbiyu da ta haifa ya sayar a N150,000


  Rundunar yansandan jihar Anambra ta kama wani mutum mai suna Chijioke Chukwulota wanda ke da kimanin shekara 31 bayan ya sayar da Jarirai da tsohuwar budurwarsa ta haifa masa a kan kudi Naira dubu dari da hamsin (N150,000).

   

  Kakakin hukumar yansandan jihar  Anambra SP Haruna Muhammed, ya ce Chijioke ya lallabi tsohuwar budurwarsa ne zuwa gidansa, daga bisani sai ya sace Jariran mata masu watanni biyu da haihuwa. Ya sayar wa wata mata mai suna Tina Ibeato mai shekara 31 da Jariran a jihar Imo a kan farashin kudi Naira dubu dari da hamsin (N150,000) kacal.


  Haruna ya ce an kama masu laifin kuma an karbe Jariran, kuma suna cikin koshin lafiya, kazalika  an mayar wa mahaifiyarsu, yayin da wadanda ake zargi ke ci gaba da fuskantar bincike kafin gurfanar da su gaban Kotu.

   


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bayan ya kaura wa tsohuwar budurwarsa ciki, ya sace yanbiyu da ta haifa ya sayar a N150,000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama