Allah Gwani: Duba abubuwan mamaki 11 game da ƙwaƙwalwa


1] A yayin da ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa na wani ɓangare suka mutu, na wani ɓangaren na iya ɗaukar aikinsu su ci gaba da aiki. Wannan shi ne abin da ke faruwa a ƙwaƙwalwar masu shanyewar ɓarin jiki har suke iya warkewa.

2] Ƙwaƙwalwa ba ta ɗauke da maganaɗisan jin ciwo wato "pain receptors", saboda haka, ƙwaƙwalwa ba za ta iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki ke jin ciwo ba. Saboda haka ciwo daga kai na zuwa ne daga sauran abubuwan da ke kewaye da ƙwaƙwalwa, amma ba ƙwaƙwalwar kanta ba.

3] Ƙwaƙwalwa ta fi kowanne sassan jiki son kanta. Domin duk da cewa nauyinta ba ya wuce kaso uku cikin ɗari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an ba ta kaso talatin cikin ɗari (30%) na yawan jinin da zuciya ke harbawa a kowanne bugawar zuciya.

4] A mafi yawan lokuta, ɗan Adam na amfani da dukkan ɓangarorin ƙwaƙwalwarsa, saɓanin tatsuniyar da ke cewa wai ɗan Adam na iya amafani da ɗan wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ne kawai a rayuwarsa.

5] Kimanin rabin sinadaren abincin da yara ke ci suna tafiya ne wajen gina ƙwaƙwalwarsu domin koyo.

6] Kamar yadda motsa jiki ko atisaye ke ƙara lafiyar jiki, haka ma yake ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.

7] Kamar yadda tambarin babban ɗan yatsan hannunka (thumbprint) yake daban da na kowa, haka ma yadda ƙwaƙwalwarka ke aiki daban da ta kowa.

8] Saboda ƙwaƙwalwa na aiki ne da tsarin lantarki, a yayin da mutum yake a farke, ƙwaƙwalwa na iya samar da ƙarfin lantarkin da zai iya kunna farin ƙwan lantarki.

9] Kimanin kaso sittin cikin ɗari (60%) na ƙwaƙwalwa kitse ne.

10] Rashin isashshen bacci na rage kaifin ƙwaƙwalwa. Ɗan Adam yana buƙatar baccin kimanin awanni bakwai zuwa tara a kullum.

11] Ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa ba sa iya jure rashin iskar oksijin da sinadarin gulukos na fiye da mintuna biyar face sun mutu.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN