APC 2023: Jerin sunayen mutane 3 da suka shirya kwace Adamawa daga hannun PDP


Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar Adamawa na iya fuskantar kalubale wajen zarcewa a jihar a 2023 idan har shirin siyasa da shugabannin All Progressives Congress (APC) ke yi ya cimma nasara. Legit.ng ta runa cewa APC ta rasa jihar a 2019 sakamakon wani rikici da aka kasa sasantawa tsakanin tsohon gwamnan jihar, ibrilla Bindow, da wasu shugabannin jam’iyyar.


Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu yan asalin jihar da ake ganin mutuncinsu na aiki don hanin sun kwato jihar a zabe na gaba. Wadannan mutane kuwa sune babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da tsohon SSG, David Babachir. An tattaro cewa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC, tsohon gwamna Bindow, da surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Halilu (Mudi), na aiki sosai don dawo da APC a jihar.


Rahoton ya kuma bayyana cewa “Sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, wani mamba mai wakiltan Jada/Ganye/Mayo-Belwa/Toungo a majalisar wakilai, Abdulrazak Namdas, da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Babale Martins” na cikin shirin jam’iyyar na kwato jihar a 2023.


Tsohon gwamnan jihar Bindow ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri a zaben 2019. A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Da yake bayar da dalilansa na sauya sheka, 

 

Ngilari ya yi korafin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar ba ta yi masa adalci. Ya ce bada dadewa ba za a fitar da jawabin sauya shekarsa, inda ya kara da cewa wasu jiga-jigan PDP da dubban magoya bayansu za su same shi a APC.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN