Tsadar rayuwa: Buhari ya mayar da martani, ya fadawa 'yan Najeriya mafita


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen farfado da fannin noma don samar da wadataccen abinci da bunkasa tattalin arzikin kasa. Shugaban kasar ya ce mayar da hankali a fannin noma zai taimaka wajen rashin dogaron kasar da fannin danyen mai, musamman wajen kasafin kudi.


Wasu daga cikin tsare tsaren shugaban kasar na farfado da tattalin arziki sun hada da rufe iyakokin kasa domin bunkasa noma shinkafa, da dakile masu shigo da abinci kasar. "Ina kara jaddada cewa daga yanzu babban bankin Nigeria ba zai kara bayar da canji ga masu shigo da abinci ko taki a kasar ba.

 

 "Ba zamu biya ko kwabo na kudaden ajiyar waje ga masu shigo da kayan abinci ko taki ba. Maimakon hakan, zamu bunkasa manomanmu na cikin gida," cewar Buhari a ranar Alhamis.


Shugaban kasar ya kasance yana mai karfafa guiwar matasa akan su koma noma, kasancewar farashin danyen mai na ci gaba da durkushewar a kasuwar duniya. Taken gwamnatin sa ya kasance, "Dole mu ci abunda muka noma, kuma dole mu noma abunda zamu ci." Shugaban kasar ya dawo kan wannan take a makon da ya gabata. "Muna da matasa masu jini a jika da ke da burin aiki, to noma shi ne mafita ga kowa," a cewarsa.Shugaban kasar ya sha suka daga shekarar 2018 a lokacin da ya kira matasan kasar a matsayin "cima zaune". Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a ranar 18 ga watan Afrelu 2018, a taron kungiyar kasashe masu takama da kasuwanci a Westminster, ya ce matasan Nigeria na jira gwamnati ta yi masu komai. 

 

A wani labarin, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa karin farashin man fetur da wutar lantarki a wannan lokacin zai kara jefa 'yan Nigeria cikin mawuyacin hali. Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran a zantawarsa da BBC Hausa ranar Juma'a ya ce babu wani kwakkwaran dalili na kara kudin fetur da lantarki.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN