• Labaran yau


  Majalisar dokokin jihar Kaduna ta zartar da dokar dandaka ga masu fyade a jihar


   Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta zartar da dokar yi wa masu fyade dandaka.

  Majalisar ta sanar da kammala zartar da dokar mai lakabin “Kaduna State Penal Court Law No.5 of 2017” a turance.

  A bisa wannan hukuncin doka, daga yanzu duk wanda aka kama da laifin fyade kuma aka tabbatar da ya aikita hakan, to ko shakka babu, za a yi masa dandaka.

  Idan dai ba’a manta ba, a cikin watan da ya gabata ne, Matar Gwamnan Jihar kaduna, Hajiya Aisha Ummi Garba Elrufai, ta kai rokon ta gaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a kan su taimaka su yi gyaran dokar domin a yi hukunci mai tsanani a kan duk wani da aka kama da laifin aikata fyade a fadin Jihar.

  Source: Leadership Ayau
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta zartar da dokar dandaka ga masu fyade a jihar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama