Jerin manyan Malaman musulunci 5 da su ka yi Allah wadai da halin da ake ciki a Najeriya


A cikin watan Satumban nan ne gwamnatin Najeriya ta yi sabon karin farashin man fetur, bayan haka kuma kudin shan wutar lantarki ya tashi a wurare da-dama. Bugu da kari ana fama da matsanancin tashin kayan abinci da mutane su ka dogara da su. Wannan ya sa ta kai malamai, sun fara fitowa su na fadakar da hukuma.



Ga kadan daga cikin wadanda su ka yi magana game da halin da al’umma su ka shiga:


1. Ahmad Gumi 

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya tattauna da BBC Hausa a ranar Talata inda ya soki tsarin gwamnatin APC na rufe iyakokin kasa, ya ce wannan ya jawo mutane su ke fuskantar tsadar kayan abinci.


2. Lawal Shuaibu Abubakar 

 

Lawal Shuaibu Abubakar wanda aka fi sani da ‘Malam Lawal Triumph’ a wani darasi ya roki gwamnatin tarayya ta saukaka talakawa a halin da ake ciki, malamin ya yi kuka da ya ke wannan jawabi.


3. Nasidi Goron-dutse 

 

Sheikh Nasidi Abubakar Goron-dutse ya na cikin wadanda su ke wayyo Allah da yanayin da jama’a su ke ciki. Babban malamin ya ce tun da ya ke bai taba ganin al’umma su na wahala irin yanzu ba. Sheikh Bello Yabo ya soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a dalilin tsadar kayan abinci da farashin man fetur. Yabo a wani karatu da ya ke yi, ya ce gwamnatin APC ta gaza, har gara mulkin baya.

4. Bello Yabo 

 

Sheikh Bello Yabo ya soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a dalilin tsadar kayan abinci da farashin man fetur. Yabo a wani karatu da ya ke yi, ya ce gwamnatin APC ta gaza, har gara mulkin baya.


5. Sani Yahaya Jingir 

 

Dattijon malamin nan na kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa duk da shekarunsa kusan 70 a Duniya, bai taba jin labarin irin tsadar da kayan abinci su ka yi a halin yanzu ba. 

 

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa limamin masallacin ITN da ke garin Zariya, jihar Kaduna, Dr. Mustapha Isa Qasim ya yi kira ga shugabanni su zama masu tausayin jama’a. Mustapha Qasim a hudubar Juma’a ta yau, ya koka da matsalar tsaro, rashin kyawun hanyoyi, da tsadar kayan masarufi, ya ce akwai bukatar masu mulki su tausaya talakawa. Shi kuwa Dr. Saeed Yunus ya yi kira ga jama’a su komawa Ubangiji domin samun sauki.

Source: Legit




Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN