Shugaba Buhari ya ce, za su ci gaba da tabbatar da Dimokradiyya a kasashen ECOWAS


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasar sa za ta cigaba da goyan bayan dorewar dimokiradiya a yankin Afirka ta yamma wajen ganin kasashen da ke yankin sun mutunta kundin tsarin mulkin da su ke amfani da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore da ya ziyarce shi don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma yankin ECOWAS.

Shugaban Buharir ya ce suna sanya ido sosai kan halin da ake ciki a kasashen da ke shirin zabuka, kuma sun fahimci kasashen da ake zaman lafiya da kuma wadanda ake fuskantar tashin hankali, har ma ya bayyana kudirin sa na taimakawa masu fuskantar yin zabubbuka nan gaba kadan.

Shugaba Kabore da ya jagoranci kwamitin tattalin arziki da kasuwanci da kuma zuba jari na ECOWAS ya ce ya ziyarci Buhari ne domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi yankin da suka hada da hukumar hadin kai tsakanin Burkina Faso da Najeriya da kuma matsalar kasuwancin da ake fuskanta tsakanin Najeriya da Ghana da Benin da Nijar domin samo maslaha.

Kabore ya yabawa Buhari kan yaki da ‘yan ta’adda da kuma jagoranci wajen tinkarar annobar korona.
Dangane da halin da ake ciki a Mali, shugaban Burkina Faso ya ce, yana fatan ganin taron da akayi a Ghana ya haifar da da mai ido domin samun 

Source: Leadership Ayau


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN