• Labaran yau


  Shagon kayan jima'i: Kotu ta ci tarar Sanatan da ya mari wata mata N50m


   

  Wata babbar kotun tarayya ta umurci Elisha Abbo, Sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa, da ya biya miliyan N50 a matsayin diyya ga Osimibibra Warmate kan cin zarafinta. A 2019, hukumar yan sanda ta gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, kan wata tuhuma guda da ake masa na cin zarafin Warmate a shagon siyar da kayan jima’i a Abuja.


  Duk da hujja na bidiyon lamarin da aka gabatar, Abdullahi Ilelah, alkalin kotun, ya riki takardar babu kara da dan majalisar ya gabatar, sannan ya kori shari’ar. Sai dai kuma, Warmate ta shigar da karar neman yanci a gaban babbar kotun tarayya. Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, alkalin ya kama Abbo da laifi sannan ya umurce shi da ya biya mai karar miliyan N50, aridar The Cable ta ruwaito.


  Lugard Tare-Otu da Nelson wadanda suka bayyana kansu a matsayin lauyoyin Warmate sun tabbatar da hukuncin kotun a shafin Twitter. “Kun tuna wannan bidiyon sanatan Najeriya da ya mari wata matashiyar mata a shago? Toh gaskiya ta yi halinta a yau inda kotu ta ci tarar sanatan N50M. Ina farin cikin wakiltan wannan matashiya a wannan kara,” in ji Nelson.


  A wani labarin, ranar Litinin, kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Nigeria da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW). A watan da ya gabata ne wata kotun shari'a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi.

  Source: Legit  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shagon kayan jima'i: Kotu ta ci tarar Sanatan da ya mari wata mata N50m Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama