Kebbi a yau: Tattakin rundunar VGN jihar Kebbi, abin da ya faru da abin da mahukunta suka ce

 


Rundunar Vigilante group of Nigeria, VGN reshen jihar Kebbi karkashin Kwamandanta tare da manyan hafsoshi da sauran manbobinta na jihar Kebbi, sun gudanar da tattaki a kan manyan titunan garn Birnin kebbi, babban birnin jihar Kebbi da safiyar Litinin 28 ga wataan Satumba.

 

Bayanai sun ce kashi daya cikin goma na yan VGN na jihar Kebbi ne suka sami halartar wannan tattaki na yau, wanda ya kunshi mutum  1750, Sakataren kudi na VGN jihar Kebbi Kwamanda Abubakar Sambawa, ya ce VGN jihar Kebbi na da yawan akalla manbobi hamsin 50 a kowane Mazaba (Ward) da ke kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi. Ya kara da cewa kaso 90 basu sami halartar wannan tattaki ba saboda matsalar rayuwa.


Bayan kammala tattakin, jami'an VGN sun sami tarbo daga Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkar tsaro Garba Hamisu Kamba , tare da Sakataren din-din-dim kan ayyuka na Musamman a Kabinet ofis Alhaji Sufiyanu Bena, inda suka gudanar da jawabai kan habbaka harkar tsaro da inganta tsarin tafiyar da tsaro, musamman yadda VGN ke bayar da gudunmuwa domin tabbatar da tsaro a jihar Kebbi.


 Kwamandan VGN na jihar Kebbi, Lawal Muhammad Augie, ya yi cikakken bayani tare da gargadi ga yan VGN na jihar Kebbi, cewa su kasance masu yin aikinsu bisa turbar doka da oda, ba tare da sa banbancin ra'ayi, akida ko addini ba wajen tafiyar da ayyukansu.


Sakataren kudi na VGN, jihar Kebbi Kwamanda Abubakar Sambawa, ya yaba wa Gwamnatin jihar Kebbi tare da manyan ma'aikatan tsaro na ofishin Cabinet da ke Birnin kebbi, bisa taimakon motoci, babura da sauran kayan aiki da Gwamnatin jihar Kebbi ta ba VGN.


 


Sai dai Sambawa, ya yi korafin cewa wani shugaban karamar hukuma ya sa dan uwan matarsa cikin VGN kuma ya bashi mukamin Kwamanda na karamar hukuma, sai ya mika masa babur da aka ce a ba yan VGN, alhalin yaron ba dan VGN bane.


Kazalika Sambawa ya yi korafin cewa , an sami matsalar yadda wasu suka karbi babura da aka ba VGN a kananan hukumomi ta hannun shugabanin kananan hukumomi, kuma suka zo garin Birnin kebbi da wadannan babura suna yin aikin Acaba.


 


Mataimakin Kwamishinan yansanda, kuma Kwamndan yan sanda na shiyar Birnin kebbi, ACP SS Ibrahim ya wakilci Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi, wanda ya yi ingantaccen bayani kan kokari da VGN jihar Kebbi ke yi wajen bayar da gudunmuwa domin tafiyar da harkar tsaro, ya kuma yi nuni da muhimmancin sanar da yan sanda lamari kafin a dauki wani babban mataki kan lamarin tsaro.


 


Duba bidiyo tare da jawabai a kasa:
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN