• Labaran yau


  Saurin fushi da hanzarin daukar fansa, hatta akan wanda ya saba mana cikin kuskure>>Darasi 1

   


  Macijiya ce ta shiga shagon kafinta, tana kutsawa sannu a hankali, cikin rashin lura sai ta yi tuntube da zarto, wanda hakan ya ja sanadiyyar da wannan zarton ya dan karceta,


  Cikin bacin rai Macijiya ta juyo, ta kaiwa wannan zarto sara, wanda hakan ya yi sanadiyyar fitan jini a bakin Macijiya.

  kokarin neman daukar fansa, ya sa wannan Macijiya ta nannaɗe wannan zarton da nufin ta yi mika don ta karairaya shi, sai dai kuma kash! hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuwarta ba tare da wannan zarto ya ji koda kwarzane ba.

  Jan hankali:

  Sau da yawa mukan yi saurin fushi da kokarin hanzarin daukar fansa, hatta akan wanda ya saba mana cikin kuskure, kuma mu dage akan sai mun dau fansa, wanda da yawa hakan kan sanya ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya.

  Ba a kan komai ake daukar fansa ba, kamar yadda saurin fishi kan sanya muguwar nadama.

  Muyi hakuri don Allah yana tareda masu hakuri.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurin fushi da hanzarin daukar fansa, hatta akan wanda ya saba mana cikin kuskure>>Darasi 1 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama