Hotuna: Magidanta biyu sun dambace jina jina har suka mutu saboda wata mata

 

Hakim Katende daga hagu Hassan Kiwango a dama

Wasu magidanta biyu sun kashe kansu bayan sun gwabza fada da makamai a tsakaninsu saboda wata mata a garin Kayunga da ke karamin yankin Kyampisi a gundumar Mukono a kasar Uganda ranar Asabar 26 ga watan Satumba.


Wadanda suka halaka kansu su ne Hassan Kiwango mai shekara 45 a Duniya, kuma mai sana'ar sayar da Katako, da kuma Hakim Katende mai shekara 48 a Duniya wanda ke sana'ar tukin mota.


Rigima ya taso ne bayan Kitande ya zargi Kiwango da yi masa shege ta hanyar neman matarsa mai suna Dorothy Birungi, wacce take aiki a kasar Saudiya , sakamakon haka ta bar masa yayansu masu shekara 12 da 14 a Duniya.

Hakim Katende tare da matarsa Dorothy Birungi


 
Rigami ta ki ci ballen cinyewa, sakamakon haka matsalar ta kai ga Kwamitin sulhu na garin, amma suka kasa shawo kan lamarin, daga bisani matsalar ta kai gaban Limamin Masallacin garin domin nema wa mutanen biyu mafita ta hanyar sulhu.

Amma majiyarmu ta labarta cewa lokacin da ake zaman sulhu a cikin Masallaci a gaban Liman, sai Ketande cike da matsanancin fushi, ya kai wa Kiwongo hari da makami ya sare shi a wuya, hannu, da bayansa a wurare da dama, shi ma Kiwongo ya mayar da martani ya yi wa Katende mumunan rauni.

Sakamakon raunuka da suka samu ne magidantan biyu suka mutu a lokaci daban daban amma a rana daya.

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN