Mazauna Edo Su Na Yi Wa Oshiomhole Shagube –Dino Melaye


Dandazon jama’a da suka yi ta fitowa a bisa titunan birnin Benin domin nu na farin cikinsu da nasarar da Gwamnan Jihar Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP ya samu a zaben gwamnan Jihar a kan dan takaran jam’iyyar APC, Pastor Osagie Ize-Iyamu, a ranar Asabar.

Wasu daga cikin mazauna Jihar sun rika yin shagube ga tsohon gwamnan Jihar, Adams Oshiomhole, wanda ya zamana babban mai mara wa Ize-Iyamu.

Kamar yanda wani tsohon wakili a majalisar kasa daga Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, wanda shi ma ya yi ta yi wa Oshiomhole da kuma jagoran jam’iyyar ta APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu, din shagube.

Oabaseki ya sami jimillan kuri’u 307,955 wanda suka ba shi nasarar lashe zaben a kan Ize-Iyamu wanda ya tashi da kuri’u 223,619.

Obaseki ya yi takara a karkashin jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar na  shekarar 2016 a kan Ize-Iyamu wanda ya yi takaran a wancan lokacin a karkashin jam’iyyar PDP, inda Obaseki din ya cinye zaben.

Sai dai kuma Obaseki da Oshiomhole, wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar na kasa sun rabu dutse hannun riga, wanda wannan rikicin ne ya hanawa Obaseki din samun tikitin jam’iyyar ta APC a zaben gwamnan, ize-Iyamu wanda ya koma cikin jam’iyyar ta APC dab da zaben fitar da gwani na dan takarar gwamnan Jihar sannan jam’iyyar ta bas hi tikitin takaran a nan take.

Da yake bayyana farin cikinsa a bisa nasarar ta Obasekia ranar Lahadi, melaye cewa ya yi an kaskantar da Oshiomhole.

“Gaisuwa ga al’ummar kasarmu maza da mata, ina kara isar da gaisuwata gareku. Ina miko maku wannan gaisuwaar ce kai tsaye daga birnin Benin ta Jihar Edo. A baya mun kasance muna jin ana ihun Osho Baba, wanda a halin yanzun sunan ya kaskanta zuwa zuwa Osho pikin.

“Ta ya za ku zaci mutumin da yake rike da laima ya gaza cin zabe a lokacin damina? Tabbas daman ai PDP ne za ta lashe wannan zaben. APC ya ya kasuwar dai? Oshiomhole yay a kasuwar dai?”

“Duk dalolin da aka rika shigowa da su a motoci zuwa cikin Edo, sun bi ruwa,” in ji Melaye.

Hakanan wasu magoya bayan na Obaseki sun ta rera wakar cewa sai Oshiomhole ya tattara kayansa ya koma Legos ya taras da ubangidansa Tinubu su zauna can su taimaka wa juna wajen kwashe kunyar shan kashi a zabe.

Magoya bayan na Obaseki sun yi ta kiran Oshiomhole da sunaye daban-daban na shakiyanci, suna  nu na cewa ya yi masu girman kai a bayan da suka yi masa tagomashi da zabensa a matsayin gwamnan Jihar a shekarar 2007.

Wani direban mota mai suna, Lucky Godwin, ya ce. “Ai Edo ba Legos ce ba, mun shaida wa Oshio da ubangidansa cewan za su sha kunya, hakan kuma ta tabbata.

Wata yarinya daga cikin magoya bayan mai suna Rose cewa ta yi, “Wannan nasarar ta yi dadi, amma ta kuma yi wa Oshioo zafi matuka.

Source: Leadership AyauLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN