Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

 


Wasu fusatattun matasa a garin Daddara dake karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina masu zanga-zanga kan rashin isasshen tsaro da yawaitan hare-haren yan bindiga sun bankawa ofishin yan sanda da na jami’an shiga da fice (Immigration) wuta.


Wani ganau ba jiyau ba, ya bayyanawa The Nation cewa matasan sun kona tayoyin mota kuma sun tare hanyoyin shiga Jibiya daga Katsina. Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Isah Gambo, ya tabbatar da hakan. 

 

Ya ce an damke 43 cikin matasan da ake zargi. Yace: “Hukumar ta samu rahoton cewa wasu fusatattun matasa daga kauyen Daddara, karamar hukumar Jibiya sun fito kwansu da kwarkwatansu sun gudanar da zanga-zanga.”


“An kawo rahoton cewa matasan sun tare hanyar Katsina zuwa Jibiya, daidai kauyen Daddara inda suka lalata motocin jami’an tsaro da na daidaikun mutane masu wucewa a hanyar.” “Hakazalika sun kona ofishin yan sandan dake Daddara, ofishin hukumar Immigration dake Danmasani, motar sintirin yan sanda, motar wani dan sanda kirar Volkswagen Gulf III, bindigogin AK47 na jami’an kare iyaka biyu, bindiga AK47 da karamar bindiÄŸi da yan sanda.”


“Bugu da kari, matasan sun fasa gilashen motocin matafiya da dama da suka bi ta hanyar.” “Sakamakon haka, hukumar ta tura jami’an PMF hajen kuma suka samu nas arar damke mutane arba’in da uku (43) cikinsu.”


Yace tuni an kwantar da kuran kuma za’a hukunta dukkan wadanda aka kama da laifi saboda hakan ya zama izina ga wasu. Ya bayyana cewa mutum daya ya rasa rayuwarsa kuma bincike ya nuna cewa wasu yan sumoga ne suka dauki nauyin matasan domin kawar da jami’an dake tsaron iyakar Najeriya.


Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN