'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama


 

An kashe mutum ɗaya an kuma yi garkuwa da wasu bakwai a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari garin Wasagu da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu na jihar Kebbi.


Yan bindigan sun afka garin na Wasugu a daren ranar Lahadi inda suka rika buɗe wa gidaje da mutane wuta. Wani ganau, da ya yi magana da SaharaReporters ya ce mutum uku sun jikkata sakamakon harin. "Sun afka garin misalin ƙarfe 7 na dare suka fara harbe-harbe, mutum uku sun samu munanan rauni.


"Ɗaya daga cikin mutane ukun ya mutu yayin da sauran biyun sunan can suna karɓar magani a Cibiyar Lafiya ta Wasugu. "Yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane a garin mu yayin da wasu suka ruga gidajensu suka rufe kofofi.


"Bayan harin, mun gano cewa sun sace mutane biyar," a cewar wani mazaunin garin Aliyu. Ya ce duk da cewa a yanzu an samu lafiya a garin, mutane da dama suna zaman fargaba ne.


Ya ƙara da cewa har yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalan wadanda suka sace ba kan batun biyan kudin fansa. A wani labarin daban da Legit.ng ta wallafa, mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin Epe da wata mota ta yi daga gadar Berger a jihar Legas.


The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020.

Source: Legit Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN