Mailafiya ya ce rayuwarsa na cikin babban hatsari sakamokon gayyatar DSS karo na 3


Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya ce rayuwarsa tana cikin garari tare da hatsari. Mailafia ya sanar da hakan ne a yayin da yake martani a kan gayyatar da jami'an tsaro na farin kaya suka yi masa a karo na uku. Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin, a wata takarda da ya fitar a Jos a ranar Juma'a, ya kwatanta gayyatar DSS da siyasa. Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su yi masa addu'ar kariya.Ya ce, "An kira ni a karo na uku da in bayyana a gaban jami'an tsaro na farin kaya da ke Jos wannan Litinin mai zuwa, 14 ga watan Satumba da karfe 11 na safe. "Baya da irin gwagwarmayar da muke yi a kotu, lauyana ya bayyana a gaban babbar kotu da ke Jos a ranar Juma'a. "Na kwashe sama da shekaru 20 ina aiki a kasar ketare a matsayin malami, ma'aikacin banki da kuma ma'aikacin gwamnati ba tare da wani mugun tarihi ba. "Bani da wani mummunan tarihi ko kadan.Amma abun takaici shine yadda a kasata ake bincikata da mugun laifi mai cike da siyasa a ciki." Ina barar addu'arku. Ina da dalilan da suka sa nace rayuwata tana cikin hatsari, kuma wasu 'yan siyasa ne suke son kashe min baki na har abada saboda fadin gaskiya. "Saboda magana da nayi a kan wadanda suka yi shahada. Dubban kananan yara, mata, dattawa da matasa da aka kashe a kasata. “Ina kira ga jama'ar da ke Jos ko wadanda za su iya zuwa Jos da su zo da yawansu domin bani goyon baya a ranar Litinin da karfe 11 na safe.Amma kada wanda ya wurga koda dutse ne a madadina. Ina muku fatan alkhairi," yace. A wani labari na daban, Legit.ng ta bayyana cewa, Dr Mailafia ya sanar da cewa wani gwamnan arewa ne yake daukar nauyin Boko Haram. Lamarin da yasa hukumar jami'an tsaro ta farin kaya suka gayyacesa domin neman karin bayani

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN