• Labaran yau


  Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade


  Daga cikin kokarin tabbatar da ingancin a fannin wutar lantarki a fadin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu manya daga makusantansa a cikin kwamitin inganta wutar lantarki na shugaban kasa (SPVPPI). Shugaban kasar ya amince da sabbin nade-naden a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2020 kamar yadda yake kunshe a wata takarda da ta fito daga ofishin ma'aikatar shari'a.  Mambobin kwamitin sun hada da antoni janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN) da ministan kudi, kasafi da tsari, Hajia Zainab Ahmed . Buhari ya kara da nada ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, duk a cikin mambobin kwamitin na musamman. Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu, wanda ya saki takardar, ya bayyana cewa sauran mambobin sun hada da darakta janar na NBPE, Alex Okoh da Babagana Mohammed, shugaban kungiyar injiniyoyi ta Najeriya.  A yayin rantsar da kwamitin a ranar Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kwatanta sashin wutar lantarki a matsayin fanni mai matukar amfani, ya bayyana cewa zai jajirce wurin tabbatar da cewa matsalar wutar lantarki ta zama tarihi. A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Augusta, ya nada Adamu Adaji a matsayin darakta janar na NBC.  Kamar yadda takaradar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya saka hannu, nadin Adaji ya fara aiki daga ranar Juma'a, 7 ga watan Augustan 2020. Shugaban fannin yada labarai na NBC, Ovuakporie Efe, ya bayyana cewa wannan sabon nadin da aka yi wa shugaban zai kwashe shekaru hudu a wannan kujerar.

  Source: Legit  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama