• Labaran yau


  Kwamishinan yan sandan jihar Lagos Haleem Odumosu ya Angonce da sabuwar Amarya


   

  Kwamishinan yan sandan jihar Lagos Haleem Odumosu, ya auri Folashade Omotade, yar kasuwa kuma Jaruma.

  An gudanar da bikin auren a Tsibirin Banana wanda ya sami halarcin yan uwa da abokan arziki ranar Asabar.

  Fitaccen Mawakin Yarbawa Shina Peters mai salon wakar Juju ne ya gwangwaje wakarsa a wajen bikin.

  Haka zalika fitaccen dan Jaridan bukukuwa Dele Momodu,  yana daga cikin wadanda suka halarci bikin

  An nada Odumosu, mai shekara 58 a Duniya, a matsayin Kwamishinan yansanda a watan Nuwamba 2019.

  Bayanai sun ce Amaryarsa ta taba yin aure, ta auri Olaseni Omotade wanda tsohon Sakataren din-din-dim na tarayya ne, wanda ya mutu a wani hatsarin Jirgin sama na Bellview 210 a ranar 22 ga watan Oktoba na 2005.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwamishinan yan sandan jihar Lagos Haleem Odumosu ya Angonce da sabuwar Amarya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama