• Labaran yau


  Kuma dai: An sake ceto yaro da mahaifin shi ya kulle a cikin Keji har shekara 2 a Katsina

  Rundunar yansandan jihar Katsina ta ceto wani yaro dan shekara 16 mai suna Sadiku Umar bayan mahaifinsa ya daure shi shekara 2  cikin Keji.

  Wani makwabcin gidan su yaron ya ce, mahaifin Umar ya daure shi tun yana da shekara 14 a Keji kuma yana ciyar da shi kamar Kare.

  Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Save the child international SCI ce ta kai rahotu wajen yan sanda bayan an rada mata halin da yaron yake ciki.

  Wakilin SCI a garin Daura Aminu Gambo, ya ce, " Mahaifin yaron ya gaya wa yan sanda cewa ya sa yaron a cikin Keji ne domin babu wajen da zai sa shi a daki biyu da ke gidansa,wanda jama'ar godan mutum  15 tare da yayansa 12 suke kawana a ciki".

  "An kulle mahaifin yaron a caji ofis na yan sanda da ke Daura na kwana daya, daga bisani aka kai shi Shelkwatar yan sanda da ke Katsina. Sai dai an sallame shi bisa sharadi da yan sanda cewa zai kula da yaron kamar yadda ya kamata kuma ba zai sake cin zarafin yaron ba".


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kuma dai: An sake ceto yaro da mahaifin shi ya kulle a cikin Keji har shekara 2 a Katsina Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama