Aikin soja a NDA: Matakan da za ku bi don samun aiki a rundunar sojan Najeriya

Kwalejin horas da manyan sojoji ta NDA a Najeriya ta fitar da sunayen waÉ—anda suka ci jarabawar karatun aikin soja tare da sanar da ranar da za a tantance su.

Sanarwar da Birgediya Janar Ayoola Aboaba, Rijistaran NDA ya fitar a ranar Laraba na Æ™unshe da sunayen waÉ—anda suka ci jarabar a dukkanin jihohin Najeriya 36 haÉ—i da Abuja. 



Sanarwar ta ce za a fara tantance waÉ—anda suka ci jarabawar ne daga ranar Asabar 12 ga watan Satumba zuwa 24 ga Oktoba a kwalejin da ke Kaduna.

Kuma an rarraba jihohin zuwa gida uku da kuma ranakun da za su halarci NDA domin tantance su.
Za a fara tantance kashi na farko na jihohin a ranar 12 ga watan Satumban 2020 kuma jihohin sun haÉ—a da: Anambra da Bauchi da Delta da Edo da Ekiti da Enugu da Gombe da Kano da Kaduna da Nasarawa da Ondo da kuma Filato.

Kashi na biyu na jihohin kuma za a tantance su ne a ranar 26 ga Satumba kuma sun haÉ—a da: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Benue da Imo da Katsina da Kogi da Osun da Oyo da Rivers da Yobe da kuma Zamfara.

Kashi na uku na jihohin kuma za a tantance su ne a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba kuma sun haÉ—a da: Bayelsa da Borno da Cross River da Ebonyi da, Abuja da Jigawa da Kebbi da Kwara da Lagos da Neja da Ogun da Sokoto da kuma Taraba.

Sanarwar da NDA ta fitar ta ce babu wata dama ga duk wanda ya yi kuskuren halartar wurin tantacewar a ranakun da aka sanar.

Ga yadda za ku nemi shiga NDA

NDA, makaranta ce gaba da sakandare kuma duk wanda zai shiga aikin makarantar ta soja ta NDA sai ya kammala karatun sakandare kuma ya ci jarabawar kammala sakandaren.

Kuma akwai adadin yawan ɗaliban da ake ƙayyadewa duk shekara, kamar a bana ɗalibai 80 aka kira.
Kafin shiga NDA sai ɗalibi ya jarabawar shiga jami'a ta Jamb kuma ya saka NDA a matsayin zaɓinsa na farko.

Akwai kuma adadin makin da ake son É—alibi ya samu a Jamb kafin shiga NDA. ÆŠaliban fasaha da sadarwa da kuma tsaron Intanet da sauransu sai sun samu maki 210.

ÆŠaliban kimiya da siyasa da tattalin arziki da sauran fannoni sai sun samu maki 180 a Jamb.
Waɗanda suka ci makin da ake buƙata za a kira su sake rubuta jarabawar shiga NDA.

Idan É—alibi ya ci jarabawar za a kira a tantance shi gaban kwamitin NDA. Za a tantance takardunsa na makaranta.

Za a kuma lafiyarsa da cancantarsa a kuma tabbatar da ba ya da wata nakasar jiki.

Idan É—alibi ya tsallake matakin tantancewa, za a kira shi horo na musamman na guje guje da tsalle tsalle domin tabbatar da cancantarsa a aikin soja.

Idan ɗalibi ya tsallake matakin tsalle tsalle da guje-guje zai kuma fuskanci wani kwamiti mataki na ƙarshe da za a zaɓi waɗanda suka fi ƙwazo.

Sauran abubuwan da ake buƙata

Ana son É—alibi ya zo da kwafi biyu na takardunsa na makaranta da kuma takardar shaidarsa ta JAMB da ya rubuta.



Ana son É—alibi ya zo da shaidar takardar fom da ya cike na NDA da kuma katin jarabawar tantancewa. 

Takardun makaranta da ake son ɗalibi ya zo da su sun ƙunshi jarabawarsa WASSCE ko NECO da takardar shaidar kammala sakandare da Firamare.

Takardar shaidar haihuwa da takardar shaida daga ƙaramar hukumar inda ɗalibi ya fito mai ɗauke da sa hannun sakararen gwamnati ko kuma shugaban ƙaramar hukuma.

Sai ɗalibi ya samo takardar shaida daga wani soja wanda ya kai muƙamin Laftanal Kanal na sojan ƙasa ko sama, wanda za a iya amfani a madadin takardar shaidar ɗan kasa daga ƙaramar hukuma (Indigeneship)

Kuma sai jami'in sojan ya bayyana matsayinsa a wasikar da adireshinsa da numbar wayansa da kuma Imel. Sai kuma ya buga tambarinsa.

Kuma É—alibi sai ya gabatar da fom da zai sauke a shafin intanet na NDA da iyayensa ko masu kula da shi za su cike kan amincewarsu da shiga aikin soja.

Duk dalibi da ya kasa kawo takardun da ake buƙata ba za a saurare shi ba kuma za a kore shi.
Duk wani Gyara da aka yi wa wata takarda zai kai ga korar É—alibi.

Kayayyakin da ake son É—alibi ya zo da su:
  • Kayan rubutu
  • Gajeren wando shuÉ—i guda uku da riga fara (T-shirts)
  • Takalmi fari Kanbas da safa farare guda uku
  • Kayan wanka soso da sabulu
  • ÆŠalibi zai biya N2,500 na tabbatar da jarabawarsa ta WAEC/NECO
  • Katin diba jarabawar WAEC da NECO
  • Lambar BVN da lambar asusun banki
  • Hotunan fasfo guda hudu
  • Takunkumi 
Source: BBC

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN