• Labaran yau


  Gaba daya fasinja sun mutu bayan motar bas ta yi hatsari ta kama da wuta

  Mutane da ba tantance adadinsu ba sun mutu bayan sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane mutum ba , bayan motar bas mai daukan mutum 18 da suke ciki ya yi hatsari ya yi ta mulmula a kasa kuma ya kama da wuta a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ranar Lahadi.


  Mutum kwaya daya tilau da motar ta jefo waje lokacin da take mulmula a kasa shi ma ya mutu, kuma an kai gawarsa wani Asibiti da ke kusa, inda aka aje gawarsa a dakin aje gawaki a cewar hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC.


  Kwamandan hukumar FRSC na jihar Anambra, Andrew Kumapayi ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin Amoka, a kan tagwayen hanyar Onitsha zuwa Owerri.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gaba daya fasinja sun mutu bayan motar bas ta yi hatsari ta kama da wuta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama