Abin da Dr. Pantami ya fada lokacin da Gwamnatin PDP ta kara kudin mai (Bidiyo)

Wani tsohon bidiyo na mai girma ministan sadarwan Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya shiga hannunmu inda aka ji ya na sukar gwamnatin tarayya a da. Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya na rike da kujera gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kuma har masana sun ce ya na cikin wadanda su ka fi kowa aiki. A wannan tsohon faifen da yanzu ya ke zagaye shafukan sada zumunta da yanar gizo, an ji Mai girma Isa Ali Ibrahim Pantami ya na sukar gwamnatin PDP.

Ministan ya yi Allah-wadai da yadda aka kara farashin man fetur a Najeriya, wanda duk da haka ana ikirarin cewa ana yi wa Talaka sauki ta biyan kudin rarar mai. Za a ji tsohon malamin jami’ar ya na sukar yadda manyan kasa su ke shan wutar lantarkin da ba a dauke ta, a daidai lokacin da mutanen kasa su ke zaune cikin duhu.


Dr. Pantami mai shekaru 46 a yanzu, ya kuma yi kaca-kaca da kudin da gwamnati ta ke da’awar ta na kashewa a matsayin tallafi domin rage tsadar fetur a gidan mai. Bayan tsadar fetur, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce hukumomi da jami’ai su na bi su na karbar kudi a hannun ‘yan acaba da masu motar haya da ke neman na abinci.


Ministan na yau ya zargi gwamnatin bayan da yin sama da kudin rarar mai da ake tarawa, ya ce wani zai lamushe wannan kudi ba tare da an yi wani abu ba. Ga abin da Ministan ya ke fada a wannan bidiyo na rabin minti: “A tunaninsu, sun ma dauka wannan wutar kamar hasken rana ce ba a dauke ta.” “Amma N2.7tr kuma a haka tallafin mai ne, a haka ana kara kudin mai, talaka ya kara shiga cikin matsatsi, kuma a haka ake tatsar ‘dan acaba, mai opel an tatse shi, a kullum za a ci N200, N300.”


Malamin addinin musuluncin ya kara da cewa: “A haka a tara biliyoyi, kuma wani ya hau kansu ya kwanta.” Wani bincike ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 6.35 a wajen biyan tallafin man fetur a lokacin Goodluck Jonathan, abin da Buhari ya soke yanzu.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN