• Labaran yau


  An Kaiwa Gwamna Zulum Hari A Karo Na Uku


   

  Rahotanni sun tabbatar da an farmaki gwamnan ne a yau Lahadi, 27 ga watan Satumba, sa’o’i 48 bayan farmakin Monguno.

  Sai dai ba rasa rai ba, kamar yadda majiyar ta bayyana. ‘Yan ta’addan Boko Haram sun sake kaiwa ayarin motocin gwamnan wadanda ke a hanyarsu ta dawowa daga yankin Monguno zuwa Maiduguri.

  Harin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan yan Boko Haram sun kai wa motocin gwamnan hari a kan hanyar Kauwa zuwa Baga, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

  Garin Monguno wanda ke da nisan kimanin kilomita 80 zuwa Maiduguri. Har ila yau garin na dauke da dubban yan gudun hijira wadanda mafi akasarinsu sun fito ne daga garuruwan Marte, Baga, Kukawa, Dikwa da sauran kananan hukumomi da ke kewaye.

  Source: Aminiya  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An Kaiwa Gwamna Zulum Hari A Karo Na Uku Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama