Kame da aka yi min siyasa ce kawai domin bata da tushe - Abubakar Dantabawa


Hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, watau Abubakar Dantabawa da ‘yansandan suka kama ranar 13 ga watan Satumba bisa zargin ganawa da ‘yan bindiga yayi martani.Daily Nigerian ce dai ta kawo Rahoton inda ta ruwaito cewa an kama Dantabawa bisa taimakon kyamarorin CCTV da gwamnan jihar, Bello Matawalle ta saka a babban birnin jihar na Gusau.Saidai a Martaninsa, Dantabawa yace mutanen da aka gani a gidansa wakilan wanda ambaliyar ruwan ya shafane da za’a baiwa taimako.

 

Yace zargin bashi da tushe ballantana makama kuma cike yake da siyasa.Yace da ‘yansandan suka shiga gidansa da misalin karfe 9 na dare sun kamashi tare da wasu abokansa 16 wadanda manyan sakatarorin gwamnati ne da ‘yan jam’iyyar PDP 

 

Ya tambayi cewa a yanzu su waye ake zargi, manyan sakatarorin gwamnatinne ko kuwa?Jihar zamfara dai na shan fama da hare-haren ‘yan Bindiga musamman barayin shanu.Saidai kungiyar gamayyar kungiyoyin fafutuka na arewa, CNG ta bakin kakakinta, Abdulaziz Saiman ta nemi da a sake Kama Dantabawa saboda ci gaba da Bincike. 

 

Daily Nigerian ta ruwaito sanarwar da kungiyar ta fitar na cewa akwai hannun wasu manya daga sama a sakin Dantabawan.

hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN