• Labaran yau


  Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana


  Chisom Dike, mamba mai wakiltar maxabar Tai, Oyigbo, da Eleme a majalisar wakilai ya bar jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar APC. Yayin da ya ke tabbatar da komawarsa APC a gaban manema labarai, Dike ya bayyana cewa ya mayar da kyautar motar alfarma da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya rabawa mambobin majalisar tarayya daga jihar.


  Ya bayyana cewa ya zabi mayar da kyautar motar ne saboda yadda gwamnatin Wike ta yi watsi da matsalolin mutanen mazabarsa. Dangane da dalilin komawarsa jam'iyyar APC, dan majalisar ya ce gwamna Wike ya ki yarda su gana domin tattauna matsalolin jama'arsa. A cewar Dike, gwamna Wike ya matukar bashi mamaki yayin da ya fada masa cewa bai sanshi ba a lokacin da suka hadu.


  "Bani da ikon ganawa da gwamna domin tattauna matsalolin jama'ar da nake wakilta. "Mun taba haduwa a baya, amma abin mamaki, sai ya ce bai sanni ba. Jin hakan ya matukar girgizani, saboda na bautawa jam'iyyar PDP tukuru lokacin yakin neman zabe. "Shi (Wike) ya taka muhimmiyar rawa wajen samun tikitina na takara, na fahimci cewa bakar magana ya fada min kuma na fahimci sakonsa "Na tuntubi ma su ruwa da tsaki da magoya bayana kafin na yanke shawara.


  Ba ni da wani sauran amfani a PDP, dole na nemi kwanciyar hankali a wani wurin daban."Ban taba samun kwanciyar hankali ba a jam'iyyar PDP, saboda sharrin makiya da ke zuga gwamna koda yaushe, hakan ne ma dalilinsa na kin yarda mu hadu," a cewar Dike.


  A cewar Dike jama'ar da ya ke wakilta suna cikin mawuyacin hali saboda rashin kyawawan hanyoyin sufuri. Dike ya kara da cewa akwai manyan jami'an gwamnatin jihar Ribas da suka fito daga mazabarsa amma sun gaza mayar da hankali wajen kawo cigaba a yankin.


  "Babu hanyoyi ma su kyau a kananan hukumomin mazabata, tafiyar minti 30 za ta dauki mutum tsawon sa'a biyu saboda lalacewar hanyaoyin ababen hawa."Duk kokarina na son ganawa da gwamna domin tattauna matsalolin jama'a bai samu shiga ba, ba ya son ganina, ba ni da wani sauran amfani a wurinsa," a cewar dan majalisar.

  Source: Legit



  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama