• Labaran yau


  Da Dumi-Dumi Daga Zaben Edo: An girke ‘yansanda 300 a kofar Otaldin da Gwamna Wike ya sauka


  Rahotanni daga jihar Edo na cewa ‘yansanda sun yiwa otaldin da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya sauka a garin Edo.Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Rivers, Ambasada Akawor Desmond ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.

   

  Yace aiki ne ya kai Gwamna Wike jihar Edo kamar yanda Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Kano da Hope Uzodinma na Imo suke amma shi Wike an girke masa ‘yansanda 300 a bakin Otalsinsa yayin da sauran kuma an barsu suna walwalarsu yanda suka ga dama.

   

  Yace mutanen jihar Rivers ba zasu taba yadda ba idan wani abu ya samu gwamnansu, shugaban ‘yansandan Najeriya suka sani.

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Da Dumi-Dumi Daga Zaben Edo: An girke ‘yansanda 300 a kofar Otaldin da Gwamna Wike ya sauka Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama