Gadar garin Margai wanda ya hada garin Kebbe da sauran sassan jihar Sokoto ya rufta sakamakon ambaliyar ruwa ranar Talata 8 ga watan Satumba.
An gina gadar ne zamanin tsohon Gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa.
Hanya daya da ta rage wa mazauna wannan yankin ita ce hanyar da ta hada garin da garin Jega wacce ke jihar Kebbi, kuma hanyar na da tsawon fiye da Kilomita 100 daga birnin Sokoto.
Malam Anas Dukura, haifaffen garin Kebbi, ya ce ana fargaban cewa dalibai da dama za su iya rasa rubuta jarabawar WAEC, sai fa idan an yi wani abu da gaggawa kan lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/