• Labaran yau


  Dauda Kahutu Rarara: Ba zan sake yi wa Buhari waƙa ba sai talakawa sun ba ni naira dubu ɗai-ɗai


  Fitaccen mawakin siyasa nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya waka, ya ce ba zai sake yi masa waka ba sai an biya shi.

  Rarara ya shaida wa BBC cewa zai sake yi wa Shugaba Buhari waka ne kawai idan talakawan da suka zabe shi kowannensu ya mika masa ₦1000.

  "Talakawa masoya Buhari na ainihi wadanda kuma akwai su, su ne za su ba ni naira dubu ɗai-ɗai sannan zan yi wa Buhari waka," in ji mawakin.

  Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon yadda ake yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Shugaba Buhari ya gaza a mulkinsa shi ya sa ya ce ba zai sake yin waka don talakawa su ji dadi ba sai sun biya kudi.

  Dauda Rarara ya kara da cewa har yanzu yana goyon bayan shugaban kasar.

  Mawakin ya musanta cewa wasu da ke kusa da Shugaba Buhari ne suka daina ba shi kudi shi ya sa ya yanke shawarar komawa wajen masoyan Buhari na hakika don su dauki nauyin wakar da yake shirin fitarwa nan da 'yan kwanaki.

  Rarara ya yi wa shugaban Najeriya wakoki da dama cikinsu har da 'Masu Gudu Su Gudu', 'Ka Fi Su Gaskiya Baba' 'Baba Dodar', 'Sai Ka Yi Takwas Uban su Zarah' da sauransu.

  Source: BBC


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dauda Kahutu Rarara: Ba zan sake yi wa Buhari waƙa ba sai talakawa sun ba ni naira dubu ɗai-ɗai Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama