Mazauna garin Lambar Tureta mai nisan kilomita kimanin hamsin kan hanyar da ta hada jihohin Sakwkwato da Kebbi da kuma sauran jihohin arewacin Nijeriya suna fuskantar barazana daga wata karamar madatsar ruwa da ke wajen garin sanadiyyar cushewa da ta yi wanda hakan ya sanya akalla sama da magidanta dari da hamsin kaura zuwa cikin garin Tureta wadansu kuma su ka canza unguwa.
Mukaddashin Shugaban Karamar hukumar mulki ta Tureta Honarabul Hassan Muhammad Tureta ya bayyana haka a jiya Laraba yayinda ya ke zantawa da wakilinmu a garin Tureta.
Honarabul Hassan ya ce wannan karamar madatsar ruwan saboda sanin
muhimmancin ta gun jama’a ya sanya tun shekaru uku da suka wuce an sha
kai koken Cushewar ta ga gwamnatin jihar Sakwkwato amma dai ba a ci
nasara ba Yanzu haka da zarar aka yi ruwan sama maimakon ruwan ya taru a
wannan madatsar ruwan sai ya shigo gidajen mutane wanda a sanadiyyar
haka ba Wai gidaje kadai ba har wannan babbar hanyar da ta hada jihohin
arewacin Nijeriya da kuma Sakwkwato tana neman halaka sabodada zarar an
soma ruwan sama duk uzurin da mutane ke da shi sai dai su hakura har sai
bayan wani lokaci mai tsawo idan an dauke ruwan.
\
Ya kara da cewa ba matsalar madatsar ruwan sama kadai ke barazana ga
jama’ar karamar hukumar mulki ta Tureta ba har ma da ruwan sama da ya ke
akwai fadamu sosai zagayen karamar hukumar kuma babu inda ruwan bai yi
barna ba duk da ya ke babu wata sahihiyar kididdiga amma a jimlace sama
da magidanta dubu biyu ne suka rasa gidaje da kuma amfanin gona.
Bayan Jajantawa ga al’ummar da abin ya shafa ya kuma yi kira ga
hukumomin da ke da hakki da su kawo agaji duk da ya ke har yanzu dai ba
a sami labarin salwantar rayuwa ba sai dukiya mai yawa.
Yayin da wadansu ke neman mafaka a sanadiyyar ambaliya a daya bangaren
kuma wadansu kariya su ke baiwa muhallansu inda garin Makera da ke
yammacin babban Birnin jihar Kebbi ruwa ne ya dauko sabuwar hanya ya
nufo garin inda su kuma al’ummar garin musamman matasa sun fito kwansu
da kwarkwata don baiwa gidajensu kariya duk da ya ke dai ruwan har ya
soma canye wadansu gidaje da ke kusa da rafi.
Malam Usman wani matashi ya bayyana cewa ba su taba ganin irin wannan
tashin hankali ba saboda ruwan ba abinda ke iya tariyarsa saboda tafiyar
da ya ke da karfin gaske, mu na dai iya kokarin mu ne muga ruwan In Sha
Allahu bai yi barna mai yawa ba.
Ya ce dan majalisa zartaswa mai wakiltar karamar hukumar mulki ta Birnin
Kebbi Honarabul Hassan Namaroko bai yi kasa a gwiwa ba da jin halinda
su ke ciki ya zo ya ga irin yadda wajen ya ke sannan kuma ya yi
alkawarin isar da korafin inda ya dace tun kama daga matakin jiha zuwa
na tarayya.
Yanzu haka dai a jihar Kebbi kusan duk kananan hukumomin da ke kusa da
fadamu ba wacce ba a sami barazana daga ambaliya ba wacce ta tilastawa
wadansu magidanta hijira yayinda su kuma hukumomin da abin ya shafa da
wakilai da shugabanni sai kai komo su ke yi ba dare ba rana don ganin
mutane sun sami matsugunansu kafin damina ta wuce.
Source: Leadership Ayau
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/