Kotu ta daure mutum 2 wata 6 a Kebbi domin yin sojin bogin kasancewa ma'aikatan wutan lantarki


Wata Kotun Majistare a birnin Argungu na jihar Kebbi, ta daure wasu mutune biyu wata uku da kuma wata  shida a Kurkuku bisa samunsu da laifin yin sojan gonar kasancewa ma'aikatan Kampanin wutan lantarki na Kaduna. Wadanda aka yanke wa hukunci sune Mu'azu Sani da Bashir Abubakar Gado.


Mutanen guda biyu suna zaune ne a garuruwan Unguwar Male da Unguwar Gado a  karamar hukumar Argungu.

 

Kakakin Kampanin wutan lantarki na Kaduna Abdulazeez Abdullahi, ya ce an kama wadannan mutanen ne da laifin hada baki domin aikata laifi karkashin sashen na 132 na dokar Penal Code. Sakamakon haka Alkalin Kotun Majistare na Argungu, Usman Umar Bunza ya yanke masu hukunci bisa tanadin doka.


Kakakin ya kara da cewa jami'an hukumar NSCDC na Argungu ne suka damke wadannan mutane yayin da suka damfarar jama'a a garuruwan Unguwar Male da Unguwar Zamare suna karbar kudin wuta .


Mutanen biyu sun amsa laifin su a gaban Kotu, sakamakon haka Alkalin Kotun ya yanke masu hukuncin daurin wata uku a Kurkuku, ko biyan taran Naira dubu bakwai N7,000 kowannensu a kan laifin hada baki domin a aikata laifi. Da kuma daurin wata shida a Kurkuku ko biyan taran Na 10,000 kan laifin yin sojin gona.


Hala zalika Kotu ta yi umarnin wadanda aka kama da laifi su biya Kampanin wutan lantarki ta Kaduna jimillan kudi har Naira dubu sittin N60, 000, ko daurin watanni shida a Kurkuku.

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN