• Labaran yau


  Fitacciyar Mawakiyar India Asha Bhosle ta cika shekara 88 a Duniya, duba abin da ta ce


  Mashahuriyar Maawakiyar Bollywood Asha Bhosle, ta cika shekara 88 a Duniya ranar Talata 8 ga watan Satumba 2020.


  A cewar Asha " Na kammala shekaru 87 kuma na fada na 88, amma ji nake yi kamar yar shekara 40. Ina fatar za ku dauki rayuwa da sauki. Ku ci gaba da murmushi, kuma shawarata gareku shi ne, ku kasance masu budaddiyar zuciya ga jama'a da kuke tare da su. Ku isar da farin ciki ga jama'a. Na gode maku kwarai da gaske".


  Asha Bhosle ta rera dubu dubatan wakokin India, daga tsarin wakokin bauta na addinin Hindu, rayuwa, musamman na fina finan Bollywood, wacce take ajin Mawakan karni na sittin, irin su Lata Mengeshkar, Kishore Kumar, Muhammad Rafi, S.P Bulashamanyam da sauransu.

   


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Fitacciyar Mawakiyar India Asha Bhosle ta cika shekara 88 a Duniya, duba abin da ta ce Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama