An yi wa yarinya mai shekara 7 yankan rago bayan ta fito tallar tsintsiya a jihar Arewa - Hotuna


Ana zargin cewa wata matsafiya ta yi wa wata karamar yarinya mai shekara 7 mai suna Juwairiya Auwal yankan rago a cikin wani Bukka a wajen aje namun daji a Jos na jihar Plateau.

 

Rahotanni sun nuna cewa ranar Asabar 5 ga watan Satumba, wata Bafulatana ta tafi da Juwairiya tare da yayarta Fatima bayan sun fito tallar Tsintsiya a unguwar Tudun OC da ke Rikkos, a karamar hukumar Jos ta Arewa.


Fatima yayar Juwairiya ta ce " Mun hadu da wata mata Bafulatana, sai ta ce mana mu bata tsintsiya kyauta, sai muka ki, sai ta taba kawunanmu, daga nan sai kawai muka gan mu a cikin wani dakin Bukka

Ko da na bude idanuna sai na gan matar tana yanka kanwata Juwairiyya. Sai na gudu domin in nemi taimako. Sai na sami wani mutum yana karanta Jarida, sai na gaya mashi abin da ya faru.


Lokacin da muka dawo, mun tarar cewa tsohuwar ta riga ta gudu, sai mutumin ya je ya shaida wa yansanda  sai yansanda suka dauki gawar Juwairiyya suka kai Asibitin kwararru na Jos, an yanka kanwata, amma ba jinin ta a kasa ko a jikinta". inji Fatima yayar Juwairiyya.


Daga karshe, yansanda sun mika gawar Juwairiyya ga iyayenta domin a bizine ta.
 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN