Wannan matsalar ta kasance tana ci wa jama'a da dama tuwo a kwarya. Sheik Adam Albani fitaccen malami ne wanda lamarin ya matukar saka shi cikin damuwa. Wani bidyonsa da ya bayyana yana yi wa shugaban kasa Buhari 'wankin babban bargo' ya janyo cece-kuce.
A cikin bidiyon wanda ya fara da sautin murya amma daga bisani ya kare da hoto, ya bayyana cewa Shugaba Buhari bashi da amfani kwata-kwata. Ya yi fatan kada Allah ya sake gwadawa 'yan Najeriya mulki irin wannan wanda ke cike da tashin hankali.
Ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wurin bai wa rayukan jama'a da dukiyoyinsu kariya, domin kuwa hakan yana daga cikin hakkin jama'a a kan gwamnatin.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/