Bidiyon keta budurcin Amarya a Sokoto: Hisbah ta kama dan gidan dan siyasa tare da mutum 2


Hukumar Hisbah a jihar Sokoto ta kama wasu mutane uku bisa zargin yada bidiyon da ya nuna ana keta budurcin wata yarinya a kafar sada zumunta.

 

Bayanai sun nuna cewa an shirya daura auren yarinyar ne ranar 17 ga watan Oktoba, amma Angon ya fasa auren sakamakon bidiyon da ya nuna ana keta budurcin Amarya da zai aura.

 

Kwamandan Hisbah na jihar Sokoto Dr. Adamu Kasarawa ya tabbatar wa manema labarai cewa Hisbah ta kama wadanda ake zargi, kuma za ta mika su ga yansanda domin fuskantar bincike da tuhuima a Kotu.


Mahaifiyar yarinyar ta ce babban wanda ake zargi a lamarin shi ne dan wani dan siyasa, ta ce ya keta budurcin yarinyar ne tun 2017 lokacin da take da shekara 16. Ta kara da cewa yaron ya ajiye bidiyon ne har tsawon shekara 3 domin kawai ya rusa rayuwar yarinyar.


LIB ta ruwaito cewa, matar ta yi zargin cewa ta kai kara ofishin hukumar DSS da hukumar kare hakkin bil'adama na kasa a Sokoto, amma basu yi komai ba a kan lamarin.


Haka zalika ta yi zargin cewa mahaifin yaron ya yi kokarin ganin cewa ta janye zancen, kuma har da yi mata barazana a lokata da dama, duk da haka ta ki amincewa.


Sai dai bayan an tuntubi mahaifin yaron Hayatu Tafida, ya tabbatar cewa ya san da zancen, amma ya musanta yi wa mahaifiyar yarinyar wata barazana ga rayuwarta dangane da lamarin.


Yanzu dai an fasa yin auren kamar yadda aka shirya za a yi a ranar 17 ga watan Oktoba saboda bidiyo da hotunan dan gidan dan siyasan da aka gani yana keta budurcin wannan yarinya a garin Sokoto birnin Shehu

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN