Bango mai shekara 100 ya kashe matar aure a Katsina


A yammacin Juma’ar da ta gabata ce mutanen Unguwar Gafai da ke birnin Katsina, suka shiga cikin jimami sanadiyar rasuwar wata matar aure, Fatima da bangon makwabta mai kimanin shekara 100 da ginawa ya fado mata.

Wannan bango kamar yadda Aminiya ta samu labari, shi kansa magajin gidan wanda yanzu shekararsa goma da barin duniya bayan shafe shekara 80 an haife shi ne a gidan.
Fatima mai kimanin shekara 24, tana da ’ya mace, kuma bangon ya zamo sanadiyar rasuwarta ce bayan ta je unguwarsu daga gidan mijinta da ke Unguwar Sabon Gida don yin ta’aziyya.

Yadda ta rasu – Mijinta

Mijinta, Malam Muhammdu ya shaida wa Aminiya cewa: “Ina kasuwa

yayanta ya kira ni ta waya ya ce in zo bango ya fado mata ta karairaye tana Asibitin Tarayya.”

“Ina zuwa na tarar da su, sai ta kira ni da Muhammadu (sunan da tunda muka yi aure ba ta kira ni da shi ba, sai dai ta ce, Dadi).”

“Na ce, haka Allah Ya yi da ke? Ta ce, ba ni hannunka, na mika mata hannuna ta rike amma idanunta a rufe. Ni dai kawai na ji ina kuka, kuma duk mutanen da ke wurin kuka suke yi.”

“Karshe aka fitar da mu waje don likitoci su yi mata aiki. To ana cikin kokarin aikin ne Allah Ya karbi abinsa.”

Game da yadda lamarin ya faru ya ce, “An ce suna tsaye kusa da bangon ita

da ’yar uwarta Rukayya, har tana cewa ‘wannan bangon yadda yake yanzu in ya fado wa mutum ai sai Lahira’.”

“An ce akwai wani yaro da ya ce musu su kauce ga bango nan zai fado, ita Rukayyar ta ji yaron, amma Fatima Allah bai sa ta ji ba, saboda shi ne ajalin. Kuma ita kadai ya taba.”

Mijin wanda auren zumunci ne tsakaninsa da marigayiyar ya ce, “Ba ni ba, har yanzu a nan makwabtanmu akwai wadanda ba su da lafiya tunda suka ji labarin mutuwarta. Kai har wadanda aljanu suka rika bugewa an samu.”

“A hirar da muka yi da ita a ranar Alhamis kafin rasuwarta, ta rika tunawa da ’yan uwa da ’yan unguwar da suka rasu. Ina rokon Allah Ya jikanta Ya gafarta mata.”

“Tunda na aure ta ba zan ce ga wani abu na saba min da ta aikata ba. In akwai wani abin da ta yi na kuskure, na sani ko ban sani ba, na yafe mata, kuma ina rokon Allah Ya yafe mata. Ina rokon duk wanda ta yi wa wani abu na kuskure ya yafe mata.”

Yadda muka ji – ’Yan uwa

Musa Junaidu Gafai, wanda ya yi magana a madadin ’yan uwan marigayiya Fatima ya ce, “Ita ce auta a gidanmu. An haife ta ranar Juma’a, an yi mata suna ranar Juma’a, an daura mata aure a ranar Juma’a, Allah Ya karbi rayuwarta a ranar Juma’a.”

“Kuma bisa yanayin da aka ce duk wanda ya rasu ta wannan hanyar ana sa masa ran shiga Aljanna. Sannan ta rasu tana hanyar zuwa sada zumunci.

Gaskiya mun yi rashi.”

“Wani abin da za mu ci gaba da tuna ta da shi, shi ne irin yadda ta maida sada zumuncin da a da muka so bari.”

“Tun lokacin da ta fara hankali, duk inda wani dan uwa yake sai ta je wajensa. A haka muka rika bin ta. Ita ce fa karama, amma ita ta yi mana wannan jagoranci.”

Mai unguwa Zubairu Gafai, wanda lamarin ya faru a unguwarsa, ya ce, “Da ma ni ne na cewa masu wannan gida a sauke wannan bango saboda alamun da ya nuna.”

“Bango ne da ya kai wajen shekara 100 kamar yadda muka samu tarihi. To kuma ga ruwa na bi ta kusa da shi.”

“A wannan daminar, an samu ambaliyar ruwa a unguwar wanda hakan ya sa tilas wadanda ke cikin gidan suka fita. Kuma har Mai girma Gwamna Masari ya ziyarci wannan wuri a lokacin da aka samu ambaliyar.”

“Abin da nake kira ga jama’a baki daya shi ne, duk inda aka ga wata matsala, a yi kokarin shawo kanta kafin ta faru. Sannan mu rika lura da batun tsabta.”

Source: Jaridar Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN