• Labaran yau


  An kawo karar tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Oshiomhole wajen Shugaban kasa

  Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Edo, ta yi kira da babban murya ga ‘ya ‘ya da magoyanta da su shirya fita ranar zaben gwama, su kada kuri’arsu.
  Ganin zaben jihar Edo ya na kara gabatowa, PDP ta bukaci mutane su yi kokarin ganin gwamna mai-ci Godwin Obaseki ya zarce a kan mulki.
  Bayan haka, jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ja wa tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole kunne.
  PDP ta nemi dinbin magoya bayanta da su yi watsi da dabarun da jam’iyyar APC ta ke neman yi na ganin an hana miliyoyin mutane fitowa su yi zabe.
  A bangare guda, Hadimin gwamnan jihar Edo, Crusoe Osagie ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, ya na zargin APC da shirya magudi.
  Mista Crusoe Osagie ya ce tun kafin a gudanar da zabe, jam’iyyar APC mai adawa a Edo ta shirya sakamakon zaben bogi domin ta murde kuri’un jama’a.
  “Wannan tsohuwar dabara ce ta jam’iyyar APC domin a cirewa jama’a kwarin gwiwar fita su kadawa gwamna Godwin Obaseki kuri’arsu.” Inji Osagie.
  A ranar 19 ga watan Satumban nan ne mutanen Edo su ke sa ran cewa za su san wanene zai rike kujerar gwamnan jihar daga 2020 zuwa shekarar 2023.
  Mai taimakawa gwamnan ya ce APC ta gudanar da zaben somin-tabi domin ganin yadda abubuwa za su kasance, amma sun ga Obaseki ya fi su farin-jini.
  Source: Legit

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kawo karar tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Oshiomhole wajen Shugaban kasa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama