• Labaran yau


  An kama wani Jami’in Lafiya da yayi barazanar kashe shugaba Buhari

  Wani jami’in lafiya da aikin sanin makamar aiki da hukumar NAFDAC, Solomon Akuma ya shuga hannun jami’an ‘yansandan Najeriya bisa zargin furta cewa zai sa a kashe shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Abba Kyari.

  Wanine ya tambayeshi shin idan ya samu Dala Miliyan 1 me zai fara tunanin yi? Sai ya mayar da martani ta shafinsa na Twitter cewa abu na farko da zai yi shine zai dauko hayar gwanin harbi daga kasar Rasha ya kashe masa shugaba Buhari da tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Marigayi Abba Kyari.

  An tsare akuma tsawon watanni 3 ba tare da gurfanar dashi a gaban kotu ba inda daga baya kuma aka kaishi kotu ana zarginshi da laifukan ta’addanci da yiwa gwamnati bore da barazana ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari

  Sahara Reporters ta ruwaito cewa zuwa yanzu ya kwashe kwanaki 150 a daure kuma kotu ta hana belinsa inda aka saka ranar 7 ga watan October a matsayin Ranar ci gana da sauraren karar.

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama wani Jami’in Lafiya da yayi barazanar kashe shugaba Buhari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama