Makiyayin da yaso auren Hanan Buhari ya bada da gudunmawar shanu 50

A lokacin da aka ɗaura Hanan, ƴar Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, akwai yiwuwar samari da dama sunyi ta cizon yatsa don ta kubce musu. Amma banda Abdullahi Bashir mai shekaru 22 ɗan wani makiyayi daga jihar Adamawa. Ya ce yana mata fatan alheri duk da cewa babu abinda zai faranta masa rai a duniya kamar auren ta.


Ya kuma bayar da shanu 55 a matsayin gudunmawarsa duk da cewa bai yi nasara ya aure ta ba. Ya yi kokarin ya hadu da ita ido da do a baya amma hakan bai yiwu ba hakan yasa ya koma amfani da yanar gizo ya yi bidiyo ya ce zai bayar da shanu 150 a matsayin sadaki idan za ta aure shi.

Ya kan yi zancen Hanan sosai idan yana tare da abokan sa inda ya ce irin riƙon da ta yi da sana'ar ta yana burge shi dubba da cewa ta fito daga babban gida. Amma da ya gano cewa an saka mata rana da wani, ya rungumi ƙaddara ya kuma sanar da cewa zai bayar da shanu 50 a matsayin gudunmawa. "Ba nuna arziki nayi ba a lokacin da na ce zan bayar da shanu 150 a matsayin sadaki ta domin ni ba kowa bane.


"Ba kuɗin shanun na ke kallo ba sai dai darajar shanu a wurin bafulatani. "Ya fi sauƙi bafulatani ya baka kyautar Naira miliyan 1 da ya ɗauki shanunsa ya baka. "Hakan na nuna irin matukar son da na ke mata", in ji shi. Abdullahi ba irin makiyayan da suke kiwon dabbobi a daji bane, domin ƙwararren mai gina shafin intanet ne kuma mai tallata haja a intanet gashi yana sha'awar ɗaukan hoto da bidiyo.


"Ni na gina shafin Intanet na Koode Radio International, wani gidan rediyo da ke watsa labarai cikin harshen fulfulde a Abuja kuma ne ke kula da shafin. "Ina kuma nemo wa gidan rediyon rahotanni a matsayin ma'aikacin wurin gadi," kamar yadda ya fadi a wata hira da ya yi da Daily Trust. Ya ce yanzu ya mayar da hankali ne don bunƙasa shafinsa ta YouTube inda ya ke fitar da bidiyo don fadakar da ƴan uwansa fulani game da sabuwar tsarin kiwo a wuri ɗaya da ilimin fasaha.


Ya ce ya fara son Hanan ne bayan ya ci karo da hotunan ta a shafin sada zumunta tana daukan hotuna a Bauchi. Ba kasafai aka cika ganin mace na aikin ɗaukan hoto ba a arewa balle ma bahaushiya ko bafulatana. Daga nan kuma ya fara bibiyar shafukan ta na sada zumunta inda ya gano cewa ashe dukkansu biyu suna son aikin ɗaukan hotuna. Cikin ƙanƙanin lokaci abokansa sun gano irin ƙaunar da ya ke yi wa Hanan har suke masa laƙabi da Gorko Hanan, ma'ana mijin Hanan a harshen fulfulde.


Daga baya ne ya gano cewa ashe ɗiyar shugaban ƙasa ne amma duk da haka bai karaya ba sai ma ƙara bincike ya ke yi a kan ta. A cewarsa sauƙin kanta yana daga cikin abinda yasa ya ke son ta domin ko a kasashen Turai da wahala ka ga yar shugaban ƙasa na sana'ar ɗaukan hoto. Daga bisani har Abuja ya tafi da nufin ya sadu da ita ya kuma fada mata abinda ke zuciyarsa na so da ƙaunar ta da ya ke yi. Ya yi ta yawo yana shiga wuraren bukukuwa a Abuja so zai yi sa'a ya hadu da ita amma Allah bai nufa hakan ya faru ba.


Daga baya dai da gaza haɗuwa da ita ido da ido ne yasa ya yi bidiyo ya saka a intanet inda ya yi alƙawarin bayar da shanu 150 a matsayin sadakin ta. "Ina cikin amfani da dandalin sada zumunta don in samu damar yi mata magana ne sai na samu labarin an saka mata rana saboda haka sai na haƙura. "Idan da hakan bai faru ba da ba tafi Yola wurin kakakaninta domin su min hanya mu gana.


"Yanzu gashi za ta yi aure. Ina mata fatan alheri kuma ina farin cikin bayar da gudummawar shanu 50 don bikin auren," ya fadi ciki sassanyar murya. Abdullahi ya dade yana yawo wuraren biki a Abuja har lokacin da aka saka dokar kulle ta korona sanan ya koma Yola.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN