An kama mata 4 bayan sun sayar da Jariri sabon haihuwa a kan N1,500,000

Hukumar hana fataucin bil'adama ta Najeriya NAPTIP, ta kama wasu mata guda hudu bisa zargin sayar da wani Jariri sabon haihuwa akan Naira Miliyan daya da dubu dari biyar ( N1,500,000).

An gabatar wa manema labarai wadannan matan ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba. NAPTIP ta ce biyu daga cikin matan  masu suna Bernadette Ihezuo da Cecilia Onyema, ma'aikatan Gwamnatin tarayya ne wadanda ke aiki a ma'aikatar kudi da ma'aikatar gona da raya karkara na tarayya.

Yayin da mace ta uku da ta hudu, Okasi Ekeoma, yar uwar Onyema ce,  ta hudun mai suna Harrieth Nmezi ita ce Kakar Jaririn da aka sayar.wacce ke zaune a jihar Imo.

Onyema ta dauki ciki ne a jihar Imo, amma sai suka kawo ta Abuja har ta haisu, daga nan ne suka dauki Jaririn suka sayar. Daga bisani wani ya rada wa hukumar NAPTIP kan harkallar, daga bisani NAPTIP ta kama matan.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN