• Labaran yau


  A cikin Masallaci aka kama kato yana yi wa yarinya mai shekara 4 fyade

  Rundunar yansandan jihar Bauchi ta kama wani mutum bisa zargin yi wa karamar yarinya mai shekara 4 fyade a cikin Masallaci.

  Yan sanda sun kama Yusuf Bako mai shekara 50 a Duniya , wanda ke zaune a Layin unguwar Wanka a birnin Bauchi, ya kai yarinyar mai suna Hauwa Jamilu zuwa wani Masaallaci da ke unguwar Aminu, inda ya aikata mata fyade.

  An yi zargin cewa Yusuf yana cikin mutanen da Gwamnan Bauchi ya yafe masu zaman gidan kaso, kuma aka fitar da su daga Kurkuku, domin a rage cinkoso saboda matsalar cutar Korona.


  Kakakin hukumar yansandan jihar Bauchi DSP Ahmed Mohammed Awkil, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rundunar ta kama wanda ake zargi ranar Juma'a 4 ga watan Satumba, kuma wanda ake zargi ya amsa laifinsa yayin da yansanda ke masa tambayoyi.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: A cikin Masallaci aka kama kato yana yi wa yarinya mai shekara 4 fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama