1] Zuciya na fara bugawa tun kwanaki 21—23 da halittar É—an tayi a mahaifa.
2] Girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum.
3] Zuciya na bugawa sau 60 — 100 a minti É—aya yayin hutu, wato yayin da ba a wani aiki.
4] Zuciya na bugawa kimanin sau dubu É—ari (100, 000) a kowacce rana.
5] Zuciya tana harba jinin da ya kai yawan galan dubu biyu (2,000) a kowacce rana.
6] Zuciya na iya ci gaba da bugawa bayan an cire ta daga jikin mutum.
7] Zuciya na da tsarin lantarki na kanta domin buga jini zuwa sassan jiki. Saboda haka, zuciya ke aiki ba tare da karɓar umarni daga mutum ba. Wannan ya sa zuciya ke ci gaba da aiki har lokacin da ake bacci.
8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 — 190 a minti É—aya.
9] Zuciya na harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 miles), in da za a ware tsayinsu.
10] A Afirka aka fara dashen zuciya na farko a duniya. An fara dashen zuciya na farko a duniya, daga mutum zuwa mutum, a ranar 3 ga watan Disamba 1967, wato kusan shekara 53 kenan, wanda likitan tiyatar zuciya É—an Afirka ta Kudu, Dr. Christiaan Barnard ya gudanar a Asibitin Groote Schuur a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
Source: Physio Hausa
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/