Bidiyon Dino Melaye da jama'a suna yi wa Oshiomhole da Tinibu shegantaka bayan zaben Edo


Sakamakon nasarar Godwin Obaseki a kan Osagie Ize-Iyamu, Jama’a da-dama sun fito su na murna da yadda zaben gwamnan Edo ya kaya a karshen makon nan. Jaridar Punch ta rahoto cewa an samu mutanen gari da su ka rika yi wa tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, shakiyanci ganin ‘dan takararsa ya sha kashi.


Fasto Osagie Ize-Iyamu na APC ya zo na biyu a zaben ne da ratar kusan kuri’a 85, 000. Haka zalika wasu ‘yan siyasa da ke adawa da Adams Oshiomhole sun nuna farin cikinsu a fili da nasarar da gwamna Godwin Obaseki ya samu na zarcewa a kan mulki. Daga cikin masu wannan murna akwai Sanata Dino Melaye wanda ya fito a cikin wani bidiyo ya na wake-waken murnar kayin da APC ta sha a hannun jam’iyyaru ta PDP.Dino Melaye wanda ya bar APC bayan Adams Oshiomhole ya zama shugaban jam’iyya, ya dauki wannan bidiyo ne daga garin Edo, kamar yadda ya bayyana da bakinsa. Melaye bai tsaya nan kawai ba, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya na cikin na hannun daman Oshiomhole.


Da ya ke magana, Dino Melaye ya ce an kassara Oshiomhole, ya zama yaro a siyasa. “Mutumin da mu ka sani da Osho Baba ya zama Osho Pikin.” Inji tsohon sanatan. Ya ce: “Ya ka ke tunanin mutumin da ke dauke da lema zai sha kasa a lokacin damina?" Ya kara da cewa: “Motar Dalar kudin da aka kawo jihar Edo ba ta yi aiki ba.” Obaseki wanda ya bar APC zuwa PDP a watan Yuli ya dauki wani salon yakin neman zabe na Edo no be Lagos domin nuna adawa ga karfin farin jinin Bola Tinubu.


Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN